ABNA24: Firai ministan ya kara da cewa bai kamada a sake albarusai kan ‘yan kasa matasa wadanda suke neman hakkinsu ba.
Alkazmi ya bayyana haka ne a taro tare da manya-manyan jami’an tsaromn kasar a jiya Litinin, inda ya bukaci a kawo masa rahoto kan abinda ya fari a ranar Lahadi a dandalin na Tahrir a birnin Bagdaza a cikin sa’o’I 72 masu zuwa.
Har’ila yau wasu kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun bayyana cewa a zanga-zangar ranar Lahadi a dandalin Tahrir na Bagdaza banda mutane biyu da suka rasu wasu 11 sun ji rauni.
342/